Nasarar da sojojin Sudan ke samu kan mayakan RSF
January 14, 2025
Mazauna garin sun yi shagulgulan murnar kwace iko da birnin Madani da sojojin kasar suka yi daga hanun yan tawayen na RSF ke nan,wadanda sukai kaurin suna wajen gana azaba ga fararen hla da yiwa mata fyade a galibin garuruwan dake fadawa hanunsu. Tuni dasi shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bai wa rundunar sojin umarnin kadamar da farmakin ayita ta kare kan birnin Khartoum da 'yan tawayen suka fattake shi daga cikinsa watanni 16 da suka gabata.
Karin Bayani: Amurka ta zargi rundunar RSF da aikata kisan kiyashi a Sudan
A bangaren, shugaban rundunar kai daukin gaggawa ta RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, ya ce asarar da sojojinsa suka yi na rasa birnin Madani ba ya nufin an gama da su.
Tun bayan da Amurka ta sanya sunan shugaban rundunar ta RSF cikin jerin wadanda ake zarga da aikata manyan laifufukan yaki, kuma kasar Masar ta fito ta nuna aniyarta na taya sojojin Sudan murkushe 'yan tawayen, rundunar ta RSF ta fara samun koma baya, bayan da ada ta kwace kusan biyu bisa uku na garuruwan kasar ta Sudan.
Masana dai irin su Dr Labeeb Nusrah, da ke fashin baki kan lamurar kasar ta Sudan na hasashen karya lagon 'yan tawayen, sakamakon barazanar da Amurka ta yi na sanya kafar wando daya ga duk kasa ko kungiyar da ke tallafawa 'yan tawayen, a wani hanunka mai sanda ga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wace akai ammanar ita ce kanwa uwar hadi, da ke tallafawa 'yan tawayen na Sudan da kudi gami da miyagun makamai.