Sojojin Sudan sun kai hare-hare a Sudan ta Kudu
November 14, 2014Talla
Da yake magana da wani gidan rediyio mai zaman kansa kakakin rundunar sojojin Sudan ta kudu Philip Aguer. Ya ce sojojin na ƙasar Sudan sun jefa bama-baman ta jiragen sama a garin Maban da ke a yankin Nilu,inda 'yan gudun hijira kusan dubu 125 suka gujewa yaƙin da ake yi a gabashin Sudan.
To sai dai ɓangaran gwamnatin ta Sudan ya musanta zargin cewar ya kai hare-haren a makofciyar ƙasar.Wannan zargi na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin Sudan,take yin wata tattaunawa ta neman sulhu tsakaninta da 'yan tawayen yankin Nilu a ƙasar Habasha.