1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojoji Chadi sun dakile 'yan tawaye

Suleiman Babayo ZMA
May 10, 2021

Bayan shafe makonni ana fafatawa sojojin Chadi sun yi ikirarin samun nasara kan 'yan tawaye da suka kunno kai daga yankin arewacin kasar.

Afrika Tschad Konflikt  Armee Soldaten gegen Rebellen in Ziguey
Hoto: Abdoulaye Adoum Mahamat/AA/picture alliance

Sojojin Chadi sun bayyana samun galaba kan 'yan tawaye bayan shafe makonni ana fafatawa a yankin arewacin kasar lamarin da ya kai ga mutuwar Shugaba Idriss Deby a fagen-daga. Mai magana da yawun sojan ya ce nasarar za ta janyo sojojin komawa bariki. A birnin N'Djamena fadar gwamnati mahukunta sun nuna 'yan tawayen da aka sama cikin datti.

Ita dai gwamnatin mulkin sojan wucin gadi ta Chadi karkashin jagorancin Mahamat Idriss Itno wanda ya kwace madafun iko bayan mutuwar mahaifinsa ta yi alkawarin shirya zabuka cikin watanni 18 domin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya.