1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Mali sun kai wa 'yan ta'adda hari

Binta Aliyu Zurmi
September 7, 2023

Rahotanni daga Mali na cewar sojoji sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta, bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewar suna kokarin kai wani mummunan hari.

Mali Unruhen Soldaten
Hoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

A wata sanarwa da sojojin suka wallafa a shafin sadarwa na X, sun bayyana samun gagarumin nasara inda suka ce ko baya ga hallaka mayakan da dama, sun kuma lalata wata maboya da suke kera makamai tare da kona wurin kurmus.

Harin da suka ce ya kaisu ga neman wani shugaban 'yan ta'addan ruwa a jallo, da ya addabi yankin arewacin Tombouctou.

Mali na daga cikin kasashen yammacin Afirka da suka kwashe sama da shekaru 10 suna fama da matsalolin tsaro, wanda daga baya ya watsu ya zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar.

Rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta Minusma wacce ke taimakawa Mali yaki da wadannan mayakan za ta fice daga kasar a karshen wannan shekarar kamar yadda sojojin da ke rike da madafun iko suka bukata.