1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka za ta fara shirin kawo karshen yakin Sudan

Abdul-raheem Hassan
November 4, 2025

Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke kira da a kawo karshen tashin hanklali mai muni a yankin Darfur, dakarun gwamnatin Sudan, za su gana da wakilan Amurka don tattauna batun tsagaita bude wuta da mayakan sa-kai na RSF.

Sudan Khartum 2025 | Militärchef al-Burhan im Präsidentenpalast nach Machtübernahme der Armee
Shugaban sojojin Sudan, Abdel Fattah al-BurhanHoto: Sudan Transitional Sovereignty Council/Handout via REUTERS

Ganawar na zuwa ne bayan wani shirin dakarun RSF ke yi na kai farmaki a tsakiyar yankin Kordofan, bayan kwace El-Fasher, tungar sojojojin gwamnati na karshe a yankin Darfur. 

Hukumomin da ke da alaka da sojoji sun yi watsi da shawarar sasantawa da aka cimma a baya wadda a karkashinta za a cire su da dakarun da suke yaki daga tsarin siyasar rikon kwarya.

Yakin da ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da raba wasu miliyoyi da matsugunansu cikin shekaru biyu da suka gabata, yanzu haka yakin ya bazu zuwa wasu yankunan Sudan a baya-bayan nan, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar wani mummunan bala'i na jin kai.

Wakilin Trump a Afirka, Massad BoulosHoto: Karim Jaafar/AFP

Matakin da Amurka ta dauka karakshin mulkin Donald Trump na yunkurin tsagaita bude wuta a Sudan da wasu kasashen Afirka, na zuwa ne bayan da ta shiga tsakanin Isra'ila da Hama don kawo karshen yakin Gaza. Wakilin Trump a Afirka, Massad Boulos, ya tattauna da ministan harkokin wajen Sudan Badr Abdelatty a kasar Masar, sannan ya kuma gana da kungiyar kasashen Larabawa.  A yayin tattaunawar, Abdelatty ya jaddada "muhimmancin kokarin da ake yi na cimma daidaiton jin kai da tsagaita bude wuta a duk fadin kasar Sudan, wanda zai share fagen gudanar da cikakken tsarin siyasa a kasar", kamar yadda sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.

Wasu shugabannin Afirka da wakilin Trump Massad Boulos a birnin DohaHoto: x.com/US_SrAdvisorAF

A cewar kungiyar hadin kan Larabawa, Boulos ya gana da shugaban kungiyar Ahmed Aboul-Gheit inda ya yi masa bayani kan kokarin Amurka na baya-bayan nan a Sudan na "dakatar da yaki, da gaggauta isar da kayan agaji da kuma fara aiwatar da tsarin siyasa".

Kungiyar da ake kira Quad wadda ta hada da Amurka da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya, sun shafe watanni suna gudanar da harkokin diflomasiyya don sulhunta rikicin da ya shafe sama da watanni 30 ana gwabzawa a Sudan. 

A cikin watan Satumban 2025, kasashe hudu suka ba da shawarar tsagaita wuta na tsawon watanni uku, sannan a tsagaita bude wuta na dindindin da kuma mika mulki zuwa farar hula na tsawon watanni tara, amma nan take gwamnatin da ke da alaka da sojoji ta yi watsi da shirin a lokacin.