1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Sojin Taliban sun yi kurarin kakkabe masu adawa da su

September 15, 2021

Sabon shugaban rundunar sojin kasa ta Taliban a Afghnaistan Qari Fasihuddin  ya lashi takobin murkushe masu adawa da mulkin Taliban a kasar.

Afghanistan | Taliban Kämpfer in der Nähe von Kabul im Jahr 1996
Hoto: Hurriyet/AP/picture alliance

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito Fasihuddin na shan alwashin hakan a wurin wani taro da ya halarta a wannan Laraba. Kwamandan Taliban din ya ce masu yi wa Taliban bore na fakewa ne da sunan kare hakkin kabilu da dimukuradiyya, kuma a karkashin jagorancin sojojin da yake yi, ba zai bar su, su sha lalas ba.

Fasihuddin da ake wa kirari da wanda ya mamaye arewacin Afghanistan ya ce manufar masu adawa da mulkin Taliban ita ce haifarwa da kasar matsalar tsaro da jefa kasar cikin rikicin basasa. Shugaban sojan ya ce Taliban na ci gaba da kokarin kafa rundunar soji ta musamman wace za ta samar da tsaro a sassan kasar bayan rugujewar rundunar sojin kasar mai dakaru 300,000 a lokacin da Taliban ta karbe iko da kasar a watan da ya wuce.

Wannan na zuwa ne a yayin da rahotannin da ke shigo mana yanzu-yanzun ke cewa 'yan Taliban sun yi nasarar kwato kudaden da suka kai darajar Dala miliyan 12.3 daga hannun tsofaffin jami'an gwamnatin Afghanistan.