1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sojojin Turkiyya 20 sun rasu a hadarin jirgin sama

November 12, 2025

Jirgin na yakin soji ya fadi ne a kasar Georgia kamar yadda wata sanarwa da Turkiyya ta fitar ta nuna.

Har yanzu, Ankara ba ta bayyana musabbabin hadarin ba
Har yanzu, Ankara ba ta bayyana musabbabin hadarin baHoto: Eren Bozkurt/AA/picture alliance

Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta ce sojojinta 20 sun rasu a wani hadarin jirgin yakin kasar da ya auku a kasar Georgia a ranar Talata.

Jirgin mai lamba C-130 ya tashi ne daga Azerbaijan zuwa Turkiyya kafin ya yi hadarin a Georgia, lamarin da ya haddasa asaran rayuka.

Ana zaman makoki bayan faduwar jirgin soji a Ghana

Har yanzu, Ankara ba ta bayyana musabbabin hadarin ba, wanda ya kasance mafi muni tun shekarar 2020 duk da cewa ta fitar da sunayen sojojin da suka rasu.

Hukumomin Turkiyya da na Georgia sun fara bincike a wurin da hadarin ya auku a yankin Sighnaghu, Kakheti na kasar ta Georgia.

Bidiyon farko da aka gani ya nuna baraguzan jirgin a cikin ciyayi, yayin da wani bidiyon da aka yada a intanet da ba a tantance ba ya nuna jirgin yana tarwatsewa a sama kafin ya fadi yana cin wuta.

Jirgin fasinja ya yi karo da na soji a Amurka

Shugabannin Azerbaijan da Georgia, tare da Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte, duk sun mika ta'aziyyarsu ga iyalan mamatan.