Dakarun Ukraine na kai ruwa rana da Rasha
February 26, 2022Dakarun Rasha suna ci gaba da kaddamar da hare-hare a Kiev babban birnin kasar Ukraine, inda ake ci gaba da jin karar abubuwa masu fashewa, kana rundunar sojin kasar ta Ukraine ta ce sojojin Rasha sun kaddamar da sabbin hare-hare da makamai masu linzami daga cikin teku. Hare-haren sun ritsa da daruruwan mutane, yayin da mazauna babban birnin suka buya a gine-ginen gidaje da makarantu gami da karkashin kadoji.
Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar ta Ukraine wanda makomarsa ke cikin mawuyacin hali ya ce biranen kasar suna karkashin matsanancin hare-hare, bayan tun farko ya bukaci tsagaita wuta. Sannan ya ce babu gudu babu ja-da baya.
Yayin da ake ci gaba musanyen wutar dakarun Ukraine sun bayyana kakkabo jirgin saman yakin Rasha na biyu wanda yake dauke da sojojin Rasha a gari mai nisan kilo-mita 25 daga birnin Kiev fadar gwamnatin kasar, abin da wani babban jami'in leken asiri na Amirka ya tabbatar. Kawo yanzu ba a tantan ce yawan dakarun Rasha da ke cikin jiragen saman da aka kakkabo ba. Sai dai ana rade-radin lamarin ya ritsa da daruruwan dakarun na Rasha.