Soke izinin canji: neman gyara ko kassara sana'a?
March 4, 2024Tun daga Kano zuwa birnin Legas da Abuja, ana ci gaba da kame masu sana‘ar canji. Sai dai soke izinin hada-hadar kudin da babban bankin Najeriya na CBN ya sanar na zaman rikici mafi girma cikin masana'antar da ke da tsohon tarihi. Babban bankin ya zargi kamfanonin da laifuka iri-iri cikin masana'antar da ya kai ga soke izini sama da 4173, cikin 5690 da ake da su. Auwal Tudun-Wada da ke sana'ar canji a Abuja ya ce hankali na tashe cikin sabuwar manufar bankin da ke zaman irin ta ta farko.
Karin bayani:Samame a kasuwannin 'yan canji na Najeriya
Duk da cewar tun daga zamanin Murtala aka fara, amma tsohuwar gwamnatin Ibrahim Babangida ce ta kai ga halasta sana‘ar canjin tare da samar mata izinin cikin batun da ke da tasirin gaske. Sannu a hankali, masana'antar na rikidewa ya zuwa gugan karfe cikin kwaramniya kudin da tarayyar Najeriyar ke fuskanta. Umar Garkuwa da ya share tsawon lokaci cikin hada-hadar, ya ce akwai barazana mai girma bisa makomar canji a Najeriya a halin yanzu.
Karin bayani: Najeriya: Faduwar darajar Naira na kara kamari
Kokarin kassara ko kuma neman gyara, an dai dauki lokaci ana zargin masu sana'ar canji da komawa kafa ta kwashe dukiyar al'umma ko bayan halasta kudaden haramun, Kuma wankan tsarkinbabban bankiCBN a tunanin Abubakar Ali da ke zaman kwarrare ga tattalin arzikin ya ce zai taimaka wajen sauya da dama daga cikin rikicin kudin da ke barazana ga makomar kasar ta Najeriya.