1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a masarautar Sokoto

Maawiyya Abubakar Sadiq AH
June 25, 2024

Shirin majalisar Zartarwa Jihar Sokoto na yi wa dokar kananan hukumomi kwaskwarima ta yadda za ta shafi batun wa'adin zababbun shugabannin kananan hukumomi da hakimai ya janyo muhawara.

Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar
Sultan Muhammadu Sa'ad AbubakarHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

 A lokacin zamanta karo na biyar ne a wannan shekara ta 2024, majalisar zartarwa ta jihar Sokoto karkashin jagorancin gwamna Ahmad Aliyu, ta amince da wasu ayyuka da kuma gyara ga wasu tanade-tanaden dokar kananan hukumomi. Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Yusuf Muhammad Maccido wanda kuma da'ne ga sarkin Musulmi na 19 Muhammad Maccido yana cikin wadanda suka karanta jawabin ga manema labarai, kuma shi ne ya karanta batun amincewar majalisar dangane da yin gyara ga dokar kananan hukumomi, wadda za ta sauya wa'adin shugabannin da aka zaba da kuma batun ikon nada uwayen kasa da  hakimmai.

Dokar na yin baraza ga rage karfin masarautar Sokoto

Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

‘'Tsarin shi ne majalisar sarkin Musulmi ita za ta gabatar da bukata ga gwamna domin nada wadanda ake so a matsayin uwayen kasa da kuma hakimmai, to amma dokar ta shekarar 2008 ta nuna cewa dammar nadi tana ga majalisar sarkin Musulmi, yadda abin ya ke dammar nadi tana ga gwamna. Ita majalisa ta sarkin Musulmi za ta gabatar ne ga gwamna domin amincewa da kuma nadawa''.Tun bayan wannan zaman ne maganganu suka rika fitowa dabam-dabam, inda bayanai suka yi ta yaduwa a kafafen sa da zumunta masu nuna cewa gwamna na yunkurin cire sarkin Musulmi daga kan karaga saboda watakila yadda suke kallon dangantakar gwamnati da sultan

Mataiakin shugaban Najeriya ya yi kashe a kan zartas da sabbin dokokin

Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Ana kan hakan ne dai kungiyar kare hakkokin Musulmi ta MURIC ta kara a kan cewa gwamnan Sokoto na makarkashiyar tube sarkin Musulmi daga kan gadon sarauta. Shi ma mataimakin shugaban Najeriya Senata Kashim Shatima ya yi kashedi a kan wannan yunkurin lokacin da yake magana wajen taron sha'anin tsaro a Jihar Katsina.‘'Mataimakin shugaban kasar dai ya bayar da sako ne ga mataimakin gwamnan Jihar Sakoto cewa sarkin Musulmi sarki ne na Sokoto amma darajarsa ta zarce hakan.‘'Ya ce: ''Shi jigo ne wanda ke rike da masarauta da wata martaba wadda dukanmu a kasarnan muke aiki domin tabbatar da mutunta  da kuma daukakata domin kasarmu  ta ci gaba''.