1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU za ta binciki kisan farar hula a Somaliya

Abdul-raheem Hassan
August 12, 2021

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka AU a Somaliya, ta kaddamar da bincike mai zurfi kan fararen hula da aka kashe yayin ba ta kashi tsakanin sojoji da mayakan al-Shabaab.

Somalia Mogadischu | AMISOM-Fahrzeug
Hoto: DW/S. Petersmann

Rahotanni sun ce mutane bakwai aka kashe ciki har da wasu manoma da wani direban mota a lokacin da sojoji da mayakan suka budewa juna wuta a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai sojojin AU da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya, sun tabbatar da kwace manyan makaman yaki da alburusai da wayoyin salula daga mayakan al-Shabaab. Tun a shekarar 2007 AU da aike dakarunta zuwa Somaliya don taimaka wa gwamnati yaki da al-Shabaab.