1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Dakatar da Firaminista

December 27, 2021

Shugaban kasar Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed ya sanar da dakatar da Firamistan kasar Mohammed Hussein Roble daga mukaminsa.

Somalia Premierminister Mohamed Hussein Roble
Hoto: Feisal Omar/REUTERS

Dakatar da Firanministan dai ya biyo bayan musayar yawun tsakaninsa da shugaban kasa a ranar Lahadi, inda dukkan bangarorin biyu ke zargin juna kan sarkakiyar da ke tattare da zaben 'yan majalisar dokokin kasar.

A cikin sanarwar da offshin shugaban kasar ya fitar, ta ce Firaministan ba zai cigaba da rike madafun iko ba har sai an kammala bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma almubazarranci da dukiyar kasa. Sanarwar ta kuma kara da cewa mambobin majalisar ministoci za su cigaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda dokar kasa ta tanadar. 

Tun dai a safiyar ranar Lahadi ce dai offishin shugaban kasar ya zargi Roble da zama babban barazana ga shirye-shiryen zabe da kuma wuce makidi da rawa a harkokin tafiyar da mulkinsa.