Somaliya na fuskantar matsanancin fari
December 20, 2021![Flash-Galerie Somalia Flüchtlingslager in Mogadishu](https://static.dw.com/image/15368535_800.webp)
Talla
Wannan dai na zuwa ne bayan karancin ruwan saman da kasar da ke fama da rikicin ta'addanci ta fuskanta na kusan damina hudu a jere. A cewar rahoton matsalar za ta yi kamarin da za ta kai ga barin kusan mutum miliyan 5 ga bukatar agajin gagawa na abinci.
Sama da shekaru 30 Somaliyar bata taba fuskantar irin wannan hali na fari da ta shiga ba. A cewar jami'in hukumar tallafin abinci Adam Abdelmoula, kananan yara daga shekaru biyar zuwa kasa wajen dubu 300 ke cikin hadarin fuskantar karancin abinci mai gina jiki cikin watanni masu gabatowa..
A watan da ya gabata ne mahukunta a Somaliya suka ayyana wannan matsala ta fari a matsayin agaji na gagawa.