Somaliya: Mutane sun rasa rayukansu a harin Mogadishu
May 22, 2019Talla
Harin wanda aka kai a kusa da wani wurin tsayawar motoci a Daljirka da ke a wajen Mogadishu ya hada da fararan hula da kuma jami'an tsaro. Ko da shi ke ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin amma dai ana kyautata zaton cewar kungiyar Al- Shebaab ita ce ke da alhaki.