Somaliya: Mutane miliyan biyar na fiskantar yunwa
September 20, 2016Talla
Adadin al'ummar kasar Somaliya da ba su da ishashshen abin da za su ci ya karu zuwa miliyan biyar, ko kuma duk mutane hudu daga cikin al'ummar kasar goma na fiskantar wannan matsala, saboda karancin ruwan sama da aka fiskanta a wannan kasa a cewar MDD a ranar Talatan nan, wanda a cewarta yara kanana su ne rayuwarsu ke cikin hadari na rashin lafiya ko ma mutuwa.
Majalisar har ila yau ta kara da cewa wannan babban abin tashin hankali ne duba da yadda a yanzu duniya ke fama da matsaloli na fari da ambaliyar ruwa da rikice-rikice ga karuwar 'yan gudun hijira.
Dubban 'yan gudun hijira ne cikin wannan shekara sun koma kasar ta Somaliya daga sansanin Dadaab, bayan da kasar Kenya ta bayyana shirin rufe sansani baki daya a watan Nuwamba.