1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Somaliya ta kori jakadan Habasha

April 4, 2024

Somaliya ta bukaci jakadan Habasha da ya fice daga kasar tare da bayar da umurnin rufe ofisoshin jakadancin Habasha guda biyu da ke Mogadishu saboda shishigi da ta ce hukumomin Addis Ababa na yi mata.

Äthiopien Addis Abeba | Treffen AU | Somalia Präsident  Hassan Sheikh Mohamud
Hoto: REUTERS

Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan da ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta gana da hukumomin yankin Puntland na Somaliya mai cin kwarya-kwaryar 'yancin cin gashin kai, wandanda a ranar Lahadin da ta gabata suka nuna rashin amincewa da hukumomin Mogadishu tare da neman cikakken 'yancin yankin.

Karin bayani: AU ta ja hankalin Habasha da Somaliya

A baya dai kasashen biyu makwabta da ke yankin kahon Afrika, na takun saka ne kan yankin Somaliland wanda ya balle daga Somaliya tare kuma da kulla alaka da Habasha, lamarin da ya haifar da rikicin diflomasiyya mai zafi.

Karin bayani: Somaliya ta yi tir da yarjejeniyar Habasha da Somaliland

Wannan lamari ya kai manyan kasashen duniya irin su Amurka da China da kuma kungiyar AU ga yin kira ga kasashen biyu da su gaggauta yi wa tubkar hanci, don kaucewa bata kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin su.