SiyasaJamus
Samaliya: An zabi sabon shugaban kasa
May 16, 2022Talla
Da kuri'u 165 ne dai sabuwar majalisar dokokin kasar ta sahale wa Hassan Cheikh Mohamud da zama sabon shugaban Somaliya, bayan da aka tafi zagaye na biyu tsakanin 'yan takarar hudu ciki har da shugaba Farmajo da wa'adin mulkinsa ya zo karshe a watan Febrairun bara.
Tuni shugaba Farmajo ya amince da shan kaye. inda ya taya sabon shugaban murna tare da tabbatar masa da goyon baya. Somaliya ta jima tana fama da matsalolin hare-haren 'yan ta'addan Al-shebab da ke ikrarin jihadi, baya ga rikicin siyasa da na fari da suka yi kaka gida a wannan kasa da ke yankin kahon Afirka, lamarin da ke zame wa sabon shugaban wani kalubale.