1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya ta soke yarjeniyoyi da Hadaddiyar Daular Larabawa

January 13, 2026

Hukumomin kasar Somaliya sun dakatar da duk wasu huldodin diflomasiyya da suka amince da Hadaddiyar Daular Larabawa saboda zargin zagon kasa da ya gitta a tsakaninsu da ya haddasa rudani.

Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud
Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh MohamudHoto: Odd Andersen/AFP/Getty Images

Gwamnatin Somaliya ta sanar da soke dukkanin yarjejeniyoyi da take da su da Hadaddiyar Daular Larabawa, ciki har da yarjejeniyar kula da tashoshin jiragen ruwa da hadin gwiwar tsaro, tana mai zargin gwamnatin Dubai da raunana ikon kasar.

Matakin ya biyo bayan rahotanni ne da shaidu da ke nuna ayyukan adawa da gwamnati, ciki har da zargin UAE da taimaka wa wani shugaba mai neman zaman kansa na Yemen ya tsere ta kasar Somaliya zuwa Abu Dhabi.

Somaliyar dai ta ce ba za ta sake bai wa Dubai izinin aiki a tashar Berbera ba, sannan hadin gwiwa da tashoshin Bosaso da Kismayo ma an soke su.

Gwamnatin ta Mogadishu ta bayyana wannan mataki a matsayin kariya ga ikon kasa da hadin kai da ‘yancin siyasa na Somaliya.