Somaliya za ta raba fararen hula da makamai
August 14, 2014Talla
Gwamnatin Somaliya ta kaddamar da sabon shirin karbar makamai daga hannu mutane, tare da samun nasarar karbe makamai kimanin 5000. Lamarin ya haifar da musayar wuta a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar. Jami'ai sun kaddamar da aikin kafin makamai su shiga hannu mayakan wadanda suke da dangantaka da al-Qaeda.
Dakarun sun caje gidan wani jami'an soji da aka samu makamai da ake zargin za a sayar wa 'yan al-Shabaab. Tuni aka kama jami'in. Kasuwar sayar da makamai ta yi kaurin suna a kasar ta Somaliya wadda shugabannin kabilu ke tafiyarwa tun cikin shekarun 1990.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal