1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ousman Sonko na fama da rashin lafiya

Abdourahamane Hassane
August 18, 2023

Jagoran 'yan adawar Kasar Senegal Ousmane Sonko, wanda ya shafe makonni yana yajin cin abinci na cikin matsanancin hali na rashin lafiya.

Ousmane Sonko jagoran 'yan adawa na Senegal
Ousmane Sonko jagoran 'yan adawa na SenegalHoto: Seyllou/AFP

 A cewar lauyoyinsa, da 'yan jamiyyarsa da gwamnati ta rusa, Sanko ya suma a assibiti inda yake cikin mawuyacin hali na  jin jiki don haka yana bukatar kulawa ta musamman. An kwantar da ousmane Sonko a wani asibiti dake a Dakar babban birnin kasar kusan makonni biyu da suka gabata, yana dai nuna adawa ne da hukuncin da aka yanke masa kan zargin fyade wanda ya yi  watsi da zarge-zargen. Kana ya  jaddada cewa hukuncin da alkalin ya yanke na da alaka da siyasa domin a hana masa tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe a senegal a shekara ta 2024.