Sosoji a Masar sun amince da takarar Al-Sissi
January 27, 2014Sai dai wannan labari na takarar Al-Sissi wanda bai dade da kasancewa a matsayin Marshal ba, bai bada wani mamaki ba.
Abun da ake jira a halin yanzu shi ne sanarwar murabus ko shiga ritayar sabon Marshal din daga matsayinsa na soja, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta wa duk wani soja zama dan takarar shugabancin kasa a Masar.
Tuni dai tun a ranar Lahadin nan Adly Mansour, wanda Janar Sissi ya nada a matsayin shugaban rikon kwarya lokacin da aka kifar da gwamnatin Mohammed Morsi, ya sanar da cewa za a yi zaben shugaban kasar kafin na 'yan majalisar dokoki nan da watanni uku masu zuwa.
Inda ake ganin cewa wannan wani tsari ne kawai da zai bai wa Al-Sissi damar lashe zaben, sannan ya samu rinjaye a majalisar kasar da za a zaba bayan ya zama zababben shugaban kasa.
Sabili da haka ne a wannan Litinin din shugaba Mansour ya nada Janar Sissi a matsayin Marshal wanda ya fi ko wane sojan kasar ta Masar girma.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal