Sowore da takun sakar kotu a Najeriya
September 17, 2025
A Najeriya matakin shari'a da hukumar tsaro ta farin kaya ta dauka inda ta kai fitaccen dan gwagwarmayar nan Omoyele Sowere kara a gaban kotu a kan zargin ya yada bayanan da suka bata suna shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da cin zarafinsa a idon jama'a ya sanya maida murtani, a dai dai lokacin da Sowere shima ya kai hukumar kara kan taje hakokinsa na bani adama.
Takun saka
Hukumar tsaro ta farin kayan ta Najeriya ta dauki matakin shari'a ne kan Omoyele Sowere bayan gargadinsa da ya goge bayanan da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta har ma da kai kararsa ga kafofin X da na Meta, amma ya dage kan cewa yancinsa ya bayyana ra'ayinsa a kan kalaman da shugaban Najeriya ya yi a kan b atun cin hanci da rashawa.
Hukumar ta DSS dai ta shigara da karara ce a gaban babban kotu da ke Abuja tana tuhumarsa da aikata laifuffuka guda biyar. Tuni masu rajin kare hakin jama'a suka maiada murtani a kan wannan mataki.
Mallam Auwal Musa Rafsanjani shi ne shugaban kungiyar kare hakin jama'a ta Cisalac kuma shugaban majalisar gudanarwa ta kungiyar Amnesty International, wanda ya nuna takaici bisa abin da hukumomi ke yi na dakile 'yancin fadin albarkacin baki.
Cece-kuce a kafar sada zumunta
Daukan wannan matakai a kan Omoyele Sowere ya haifar da sabuwar takadama a kan batun da ake ta cece-kuce kansa a tsakanin jama'a musamman a shafukan sada zumunta. Amma a tsarin mulkin Najeriya abinda Sowere ya yi zai iya fsukantar kai shi kara a kotu? Barrister Buhari Bello lauya ne mai zaman kansa da ke Abuja yana ganin ba laifi game da cewa wani jami'in gwamnati ya yi kara, amma sauran batutuwan suna da sarkakiya.
To sai dai ga Imran Wada Nas dan gwagwarmaya a Najeriya ya bayyana bukatar kala daukacin lamarin a tsanake musamman kalaman da Sowere ya wallafa da suka tunzura hukumar tsaro ta farin kaya a Najerya.
Sowere bai yi kasa a gwiwa ba
A nasa bangaren Sowere ya maida murtnai inda shi ma ya tunkari kotu yana karar hukumar DSS da ma shafukan sada zumu ta na X da Meta kan zargin an take masa hakkinsa na dan kasa.
A yanzu dai kotunan Najeriyar ne za su zama dandali da za a tirje kasa a tsaganain Omoyele Sowere da hukumat trsaro ta farin kayan, domin bangarorin biyu sun saba da karawa da juna kan batun ‘yanci fadin albarkacin baki a Najeriya don haka jelar kura ce da ta saba da raba.