1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ana ci gaba da neman wadanda suka bata a Spain

November 2, 2024

Firaministan Spain Pedro Sanchez ya ba da sanarwar aikewa da sojoji dubu biyar da karin 'yan sanda da jandarmomi dubu biyar don taimaka wa mazauna kudu maso gabashin kasar, wadanda ambaliyar ta shafa.

Hoto: Rober Solsona/Europa Press/IMAGO

 Kwanaki hudu bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta yi barna a kudu maso gabashin Spain, firaministan ya ce  wasu sabbin dakarun soji sun isa a yankin da lamarin ya faru don taimaka wa wajen neman wadanda suka bata tare da dawo da garuruwan da laka ta bizne. Rahotannin na baya-bayan nan da hukumomin kasar suka bayar na nuna cewar akalla mutane 211 suka mutu, ciki har da 204 a yankin Valencia, inda ambaliyar ta fi yin barna. yayin da wasu mutane biyu suka mutu a Castile-la-Mancha. Sai dai hukumomin sun yi gargadin cewar wannan adadin na iya karuwa, saboda ana ci gaba da neman mutane da dama da  suka bata,