1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSpaniya

Ruwan sama ya sake yin barna a Spain

Abdourahamane Hassane
November 13, 2024

A Spain an kwashe dubban mutane tare da dakatar da layukan dogo bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a kudanci da gabashin kasar,

Spanien I Barcelona - Unwetter in Katalonien
Hoto: Kike Rincón/EUROPA PRESS/picture alliance

 Makonni biyu bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa yankin a Valence wacce ta kashe mutane sama da 200 Tun farko hukumar kula da yanayi ta  gargadi mazauna.Lardunan Malaga da Andalusia, ta kudu da Tarragona da Kataloniya ta arewa maso gabas cewar sun fice daga yankuna.A Malaga, inda hanyoyi da dama suka cika suka batse suka malala,an rufe tashoshin jiragen kasa tare da dakatar da layin dogo zuwa birnin Madrid.