1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Spain da Ireland da Norway sun amince da kasar Falasdinu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 28, 2024

Tun a makon da ya gabata ne dai kasashen uku suka amince da a Talatar nan za su dauki wannan mataki a hukumance, wanda ya janyo musu martani ma zafi daga Isra'ila

Hoto: Rebecca Ritters/DW

A Talatar nan ce kasashen Spain da Ireland da  kuma Norway suka amince da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta a hukumance, lamarin da ya fusata Isra'ila.

Karin bayani:Spain da Ireland da Norway za su fitar da sanarwar hadin gwiwar caccakar Isra'ila

Tun a makon da ya gabata ne dai kasashen uku suka tsayar da Talatar nan a matsayin ranar da za su sanar da wannan mataki a hukumance, wanda ya janyo musu martani ma zafi daga Isra'ila.

karin bayani:G20 ta amince da samar da kasar Falasdinu

Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares, ya ce sanarwar da kasashen uku suka fitar ta jaddada aniyarsu ta amincewa da 'yancin Falasdinawan, kuma ita ce matsayarsu a ko yaushe.