1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Spain Ireland da Norway sun caccaki Isra'ila kan Falasdinu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 28, 2024

Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares ya ce sanarwar da kasashen uku za su fitar za ta jaddada aniyarsu ta amincewa da 'yancin Falasdinu

Hoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Kasashen Spain da Ireland da kuma Norway za su fitar da sanarwar hadin gwiwa da kakkausar murya kan Isra'ila, bayan martani mai zafi game da amincewarsu da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa mai cin gashin kanta a yau.

Karin bayani:Falasdinawa na son Amirka ta amince da su

Ministan harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares ya ce sanarwar da kasashen uku za su fitar za ta jaddada aniyarsu ta amincewa da 'yancin Falasdinawan, kuma ita ce matsayarsu a ko yaushe.

Karin bayani:Larabawa na son a kafa kasar Falasdinawa

Isra'ila dai ta soki ra'ayin kasashen uku cikin wani martani mai zafi.