1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Spain ta toshe 'yan gudun hijira daga Moroko

May 18, 2021

Kasar Spain ta jibge sojojinta a kan iyakarta da kasar Moroko a wannan Talata don dakile ci gaba da kwararar 'yan gudun hijira daga Morokon.

Marokko Spanien | Tausende Migranten schwimmen nach Ceuta
Hoto: Javier Fergo/AP Photo/picture alliance

'Yan gudun hijirar dai, manyan su da kananan su, sun fake da matakin gwamnmati na sassauta dokokin kan iyaka ne na baya-bayan nan, inda suka rinka hawa kananan jiragen ruwa don haura zuwa nahiyar Turai.

Lamarin dai ya haifar da tankiya ta diflomasiyya a tsakanin mahukumtan Spain da Moroko, inda a cikin kwana daya, kwararar 'yan gudun hijirar ta haifar da matsananciyar bukatar agajin gaggawa ga garin Spain da ake kira da Ceuta, inda nan ne 'yan gudun hijirar Morokon su 6,000 suka yada zango. 

Da jin wannan labari, Firaministan Spain Pedro Sanchez ya katse taron da yake halarta na shugabannin Afirka a Faransa, inda yanzu ya mayar da hankalinsa ga kasar Moroko wace suke zargi da cinno wa Spain 'yan gudun hijira.