1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata

August 20, 2023

Kasar Spain ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata na bana

FIFA Kwallon kafar mata | Wasan karshe Spain da Ingila
'Yan kwallon kafar Spain sun lashe gasar kofin duniya na mataHoto: James Gourley/Shutterstock/IMAGO

Matan Spain din sun samu wannan nasarar ce bayan da suka lallasa Ingila da ci 1 da nema a wasan karshe na gasar, inda a mintuna na 29, Olga Carmona ta zura kwallo a ragar Ingilar.

Wannan ne dai karo na farko da kasar Spain ta lashe kofin duniya na mata. A yanzu dai kasar Spain na biye wa Jamus a baya na kafa tarihin taba lashe gasar kofin duniya na kwallon kafa maza da kuma mata.