1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

COVID-19: Za a fitar da kundin mutanen da ba son rigakafi

December 29, 2020

Hukumomi a kasar Spain za su tattara kundin bayanan mutanen kasar da suka bijire wa karbar rigakafin corona. Ministan Lafiyar kasar Salvador Illa ya ce za su tura wa sauran kasashen kungiyar Turai ta EU wadannan bayanai.

Spanien Impstart Senioren in Madrid
Hoto: Comunidad de Madrid/REUTERS

Sai dai ministan kasar ta Spain ya ce za su yi hakan a cikin sirri, yana mai cewa idan ana son a yi maganin corona sai kowa ya amince da rigakafin da aka fara yi a Spain a ranar Lahadin da ta gabata.


Gwamnatin kasar ta ce duk da wasu na nuna shakku kan sahihancin rigakafin amma za ta sanar da kowa lokacin da ya kamata ya je domin a yi masa ita. Spain dai na gaba-gaba a cikin kasashen Turai da corona ta fi kisa, inda kawo yanzu cutar ta yi ajalin mutum sama da 50,000.