Spain za ta sami tallafin ƙungiyar Tarrayar Turai
June 25, 2012Ƙasar Spain ta buƙaci samun agaji a hukumce ga ƙungiyar Tarrayar Turai na kuɗin da za a bata rance domin ceto bankunanta dake cikin halin durkushewar tattalin arziki.
Ko da shi ke ƙasar ba ta fayace addadin kuɗaɗen da ta ke so ba ,amma a makonnin biyun da suka gabata hukumomin na Spain,sun sanar da cewar suna buƙatar biliyan dubu 62 domin ceto bankunan,dangane da wannan sanarwa da ƙasar ta bayana, yanzu haka kuɗin ruwa ya ƙaru a kuɗaɗen basusukan ƙasar, yayin da kasuwannin hanayen jari na ƙasar suka yi ƙasa da kashi ukku.Gwamnatin ta Spain ta ce za ta fara tattaunawa da ƙungiyar Tarrayar Turan akan yawan kuɗaɗen rance da za a bata da kuma ƙaidoji da za a giciya mata kafin taron ƙungiyar ƙasashen Tarrayar Turai da za a gudanar a ƙarshen wannan wata.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Auwal