1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spaniya: Al'ummar Kataloniya ta gudanar da zanga-zanga

Gazali Abdou Tasawa MNA
September 20, 2017

Dubunnan jama'ar yankin Kataloniya na kasar Spaniya sun gudanar da zanga-zanga a wannan Talata a birnin Barcelona domin nuna rashin amincewarsu da kama wasu shugabannin yankin.

Spanien Proteste nach der Festanahme von Josep Maria Jove in Barcelona
Hoto: Reuters/A. Gea

A wannan Talatar dubunnan jama'ar yankin Kataloniya na kasar Spaniya sun gudanar da zanga-zanga a saman titunan birnin Barcelona domin nuna rashin amincewarsu da kama wasu mambobi 12 na gwamnatin yankin na Arewa maso Gabashin kasar da ke son shirya zaben raba gardama kan neman ballewar yankin daga dunkulalliyar kasar ta Spaniya, shirin da hukumomin shari'ar kasar suka haramta. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa masu zanga-zangar sun tattaru a gaban ofishin ministan harkokin wajen kasar, inda jamai'an tsaro suka ja daga. Tuni dai gwamnatin Kataloniyar ta yi tir da Allah wadai da wannan kame na shugabanninta. Carles Puigdemont shi ne shugaban yankin 'yan awaren na Kataloniya:

"Na kira taron gaggawa na wannan gwamnati tamu domin yin tir da Allah wadai da harin da gwamnatinmu take fuskanta daga jami'an tsaron ofishin ministan cikin gida na kasar Spaniya da nufin hana wa al'ummar Kataloniya zabar abin da take so."


Hukumar 'yan sandar birnin na Barcelona ta tabbatar da kame shugabannin gwamnatin 'yan awaren yankin Kataloniyan 13, a lokacin wasu jerin samame 22 da jami'an tsaron suka kai a wurare dabam-dabam a kokarin da gwamnatin Madrid ke yi na hana gudanar da zaben raba gardamar na ranar daya ga watan Oktoba mai zuwa.