Spain ta fitar da Jamus a wasan cin kofin Turai
July 5, 2024Kasar Spaniya ta kai wasan kusa da na karshe bayan doke Jamus biyu da daya a wasan da suka kammala, a gasar neman cin kofin kwallon kafa na kasashen nahiyar Turai da ke gudana a nan Jamus wato Euro 2024. An tafi hutun rabin lokaci babu kasar da ta jefa kwallo a raga. Sai dai bayan an dawo rabin lokaci, a mintuna na 51 da fara wasan Spaniya ta jefa kwallo a raga kafin Jamus ta farke a mintoci na karshe. Bayan da aka kammala mintuna 90 a wasan ana kunnen doki daya da daya. An tafi karin lokaci inda Spaniya ta kara yin nasarar jefa kwallo a ragar Jamus din a mintoci na karshe. Wannan nasara dai ta sanya kasashen biyu yin kan-kan-kan, wajen samun galaba a kan junansu. A hannu guda kuma hukumar kula wasan kwallon kafa ta Turkiyya ta ce za ta daukaka kan hukuncin hana dan wasan kasar Merih Demiral wasannin biyu saboda alama da ya nuna da hannu lokacin wasan da kasar ta fafata a zagaye na biyu.