1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SPD ta ce ba ta yi kawance da CDU ba

Ahmed Salisu
September 24, 2017

Jam'iyyar SPD ta Martin Schulz ta ce ba ta yi kawance da jam'iyyar da CDU ta Angela Merkel idan aka kai gaba ta kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Bundestagswahl 2017 | SPD - Martin Schulz, Kanzlerkandidat
Hoto: Reuters/M. Dalder

Jam'iyyar ta SPD ta bayyana hakan ne jim kadan bayan rufe rumfunan zabe da kuma bayyana hasashen farko da aka yi na zaben wanda ya bawa jam'iyyar ta SPD kashi 20 cikin 100. Martin Schulz da ya kalubalanci Angela Merkel a zaben da aka yi na yau shi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka yi da shi dazu inda ya ke cewar ba za su hada hanya ba da jam'iyyar Merkel. To sai da duk da wannan, Angela Merkel ta ce kofar jam'iyyarta a bude ta idan har SPD din ta sauya tunani gama da shawarar da ta yanke na kin yin kawance da ita.