1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

SPD za ta ayyana Scholz a matsayin dan takara

November 25, 2024

Olaf Scholz zai wakilci jam'iyyarsa ta SPD ce a zaben kasa na Jamus da za a gudanar a watan Fabrairun 2025.

Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Uwe Koch/HMB Media/piccture alliance

A ranar Litinin ne jam'iyyar shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz  za ta ayyana shi a matsayin dan takara a zaben da ke tafe a watan Fabrairun 2025 don neman sake dare kujerar da ya ke kanta.

To sai dai kuma Mista Scholz na fuskantar jan aiki a gabansa na ganin ya samu damar ci gaba da kasancewa shugaban gwamnatin Jamus.

An share wa Scholz hanya zama dan takarar jam'iyyarsa ta SPD ne bayan ministansa na tsaro Boris Pistorious ya yanke shawarar ba zai tsaya takara ba.

Shugaban gwamnatin Jamus zai sake tsayawa takara

Za a gudanar da zaben watanni bakwai kafun ainihin lokacin da aka tsara yinsa sakamakon rushewar hadakar da jam'iyyun da suka kafa gwamnati suka yi, wadanda suka hada da FDP da kuma jam'iyyar Greens.

Scholz mai shekara 66 za wakilci jam'iyyarsa ta SPD mafi dadewa a siyasar Jamus wacce ake ganin farin jinita na disashewa.

An saka ranar zabe a Jamus

Da farko wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyarsa sun nuna goyon bayansu ga Pistorious inda suke cewa Mista Scholz ya shaku da sauran jam'iyyun hadaka matuka maimakon jam'iyyarsa ta SPD.