Mbappe ya tsinci kansa cikin wata takaddama
October 28, 2026
Rahotanni na cewa kamfanonin China guda uku sun dakatar da huldarsu da Mbappé, bayan cece-kucen da suka biyo bayan bidiyon da ya yadu. Bincike ya nuna cewa yarjejeniyoyin talla da aka dakatar na iya kaiwa kimanin yuan miliyan 50 na China kimanin Euro miliyan shida da dubu dari bakwai
Lamarin ya faro ne bayan wasu kalamai da hotunan barkwanci da suka yadu a shafukan intanet, inda masu amfani da kafafen sada zumunta a China suka bayyana cewa abubuwan sun bata musu rai, tare da nuna rashin girmama al'adu da martabar al'ummarsu. Wannan ya haddasa zazzafar muhawara a tsakanin magoya bayan kwallon kafa da kuma mabiyan Mbappe a fadin duniya.
Wasanni: Matsin lamba ga shugaban FIFA Infantino
Wai me Mbappe ya yi?
A bidiyon - The Bridge - Kylian Mbappé ya yi martani kan wani hoto da aka hada fuskarsa da ta Mao Zedong, yana cewa wannan shi ne barkwancin da ya fi ba shi dariya, sannan ya ambaci mutumin a matsayin "wani dan kama-karya na China"
Matsalar ita ce Mao Zedong ba mutum ne na yau da kullum ba a China. Shi ne wanda ya kafa Jamhuriyar Jama'ar China kuma har yanzu gwamnati da mutane da yawa suna kallonsa a matsayin babban bangon tarihi. Don haka mutane da dama a China sun dauki kalaman Mbappé a matsayin cin mutunci ga tarihin kasarsu.
Gidan talabijin na gwamnatin China, China Media Group (CMG/CCTV) ya dakatar da yada wasannin La Liga da kuma tallace-tallacen da suka shafi Mbappé. Haka kuma an bayyana cewa an takaita wasu asusunsa a shafukan Weibo da Xiaohongshu.
Jami'an ma'aikatar harkokin wajen China sun bayyana cewa suna "daukar neman afuwar Mbappé da muhimmanci", amma suna sa ido kan matakan da zai dauka a gaba.
Wannan rikici ya zo ne a daidai lokacin da Mbappé ke fuskantar takaicin rashin samun kyautar lambar yabo ta Ballon d'Orna 2026, inda dan wasa Harry Kane ya lashe kyautar. Rahotanni sun nuna cewa Mbappé ya zo na biyu.
Faransa da Spain za su fafata a wasan kusa da na karshe
Masu sharhi kan harkokin kwallon kafa sun ce lamarin ya kara jan hankali daga gazawar Mbappé wajen lashe Ballon d'Or, domin maimakon a ci gaba da tattauna rawar da ya taka a kakar wasa, kafafen yada labarai sun koma mayar da hankali kan rikicin China.
Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa wannan rikici zai shafi cancantar sa ta lashe Ballon d'Or nan gaba, domin masu kada kuri'a kan fi duba nasarorin da dan wasa ya samu a fili da kuma kwazon sa a wasa. Duk da haka, masana suna ganin cewa batun mutunci da martabar dan wasa na iya yin tasiri ga yadda ake kallon sa a duniya.
Duk da cewa Mbappé ya yi gaggawar neman afuwa cikin harshen Faransanci, Turanci da Sinanci, rikicin ya riga ya haifar masa da asarar wasu kwangilolin talla da aka kiyasta darajarsu zuwa kusan Euro miliyan 6.7, tare da jefa makomar wasu yarjejeniyoyinsa a kasuwar China cikin rashin tabbas.