Jawabin murnar bukukuwan Kirsimeti
December 24, 2019Talla
Shugaba Frank-Walter Steinmeier, ya yi kira ga jama'a da su kara karfafa tafarkin dimukuradiyya da taimaka wa juna a cikin yanayi na hulda mafificiya, a yayin jawabinsa na sakon taya murna zuwa ga al'ummar kasar kan bukukuwan Kirsimeti. Shugaban ya kara da cewa bayan harin da ya auku a wata majami'ar Yahudawa da ke Halle, lokaci yanzu na kara hadakanmu ba tare da wani bambanci ba a tsakaninmu.