Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya fasa zuwa Ukraine
October 20, 2022Talla
Tun daga farko dai an sanar da cewa Shugaba Steinmeier zai yi tozali da takwaransa na Ukraine Volodymyr Selenskyj a birnin Kiev, sai dai kuma luguden wuta ba kakkautawa da Rasha ke yi a wasu manyan biranen Ukraine ciki har da Kiev sun haddasa dage tafiyar, ko da yake kakakin shugaban kasar da jakadan Ukraine a Jamus, sun bayyana a shafinsu na Twitter cewa kasashen Ukraine da Jamus na da anniyar tsara wata muhimmiyar ziyara nan da gaba, duk da yake ba su yi wani karin haske ba a kai. Ana sa ran shugabanin biyu na Jamus da Ukraine za su tattauna ta wayar tarho a wannan Alhamis.