1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

STRUCK YA KAI ZIYARA A ISRA'ILA

YAHAYA AHMEDJune 8, 2004

A jiya ne ministan tsaron tarayyar Jamus, Peter Struck, ya fara wata ziyarar aiki a Isra’ila, inda ya yi shawarwari da Firamiya Ariel Sharon, da takwarar aikinsa na Isra’ilan, Shaul Mofas, da kuma shugaban kasar Moshe Katsav. Ban da batutuwan da suka shafi huldodi tsakanin kasashen biyu a fannin soji, ministan ya kuma tattauna halin da ake ciki yanzu a huskar tsaro a Gabas Ta Tsakiya, da mahukuntan na Isra’ila.

Ministan tsaron tarayyar Jamus, Peter Struck, yana gaisawa da Firamiyan Isra'ila, Ariel Sharon, a loakcin da ya kai masa ziyara a ofishinsa a birnin Kudus
Ministan tsaron tarayyar Jamus, Peter Struck, yana gaisawa da Firamiyan Isra'ila, Ariel Sharon, a loakcin da ya kai masa ziyara a ofishinsa a birnin KudusHoto: AP

Wannan ziyarar dai, ita ce ta farko da Peter Struck ya taba kaiwa a Isra’ila, a mukaminsa na ministan tsaron tarayyar Jamus. Tun da dadewa ne aka shirya wannan ziyarar, amma sai yanzu ne ministan da takwarar aikinsa na Isra’ilan suka sami damar amincewa kan lokacinta. Ban da ganarawar da ya yi da Schaul Mofas, ministan tsaron na Isra’ila, Peter Struck, ya kuma gana da shugaban kasar Mosche Katsav, da Firamiya Ariel Sharon. Gundarin tattaunawar tasu dai, ya shafi halin tsaron da ake ciki yanzu ne a Gabas Ta Tsakiya. Abin da ake ta korafi a kansa a halin yanzu, shi ne sha’awar da Isra’ilan ta nuna ta sayen jiragen yaki masu tafiya karkashin ruwa daga nan Jamus. Dokokin Jamus dai sun hana gwamnati sayad da makamai a yankunan da ake ta samun hauhawar tsamari da kuma tashe-tahsen hankulla. Wannan kuwa ya shafi Isra’ilan. Sabili da hakan ne masharhanta da dama ke ganin cewa, wannan cinikin ba zai yiwu a halin yanzu ba. Kafin dai a tsai da wata shawara kan wannan batun, sai majalisar tsaro ta gwamnatin tarayya ta yi muhawara a kansa, ta kuma zartad da kuduri kan cancanta ko kuma rashin cancantar cinikin. Babu shakka, Isra’ila ta fada a yankin da ake ta hauhawar tsamari. Amma bisa cewar ministan tsaron Jamus, Peter Struck:-

"Gwamnatin tarayya ba ta da wasu shakku kan irin wannan cinikin da Isra’ila. Muna sane da bukatar da Isra’ilan ke da ita, ta samar wa kanta kyakyawar halin tsaro. Amma ba mu da wata hanyar ba ta taimako na kudade."

Wato abin da ministan ke nufi a zahiri a nan shi ne, mai yiwuwa a amince da sayar wa Isra’ila jiragen yakin. Amma gwamnati ba za ta iya rage mata ko kwabo a kan farashin Euro miliyan dari 5 na ko wane jirgi ba. A da can, lokacin da Isra’ila ta sayi wani jirgin ruwan Jamus, sai da gwamnatin tarayya ta tallafa mata da dimbin yawan kudade. Hakan dai ba zai yiwu a halin yanzu ba, inji Struck. Sabili da haka ne wani kwamitin kasuwanci na kasashen biyu, zai fara zama a cikin `yan makwanni masu zuwa nan gaba, don tattauna wannan batun. Ministan tsaron na Jamus dai ya kuma nuna sha’awarsa, ga wata fasahar makamashi da Isra’ilan ta kware a kanta. Kamar yadda ya bayyanar:-

"Isra’ila tana da matukar kwarewa a fasahar nan ta kera jiragen sama, masu tashi da kansu ba da matuka ba. A halin yanzu kuwa, kusan ko’ina a duniya, inda bukatar leko wasu yankuna daga sama ta taso, irin wadannan jiragen ne suka fi dacewa a yi amfani da su. Isra’ila tana kan gaba a jerin masu sarrafa irin wadannan jiragen, da kuma makaman da za su iya dauka. Muna dai sha’awar wannan fasahar, kuma a cikin ayyukan hadin gwiwar da muke yi, za mu takalo wannan batun."

A bayan shinge dai, har ila yau, gwamnatin tarayyar Jamus na ci gaba da taka rawarta ta mai shiga tsakani, wajen cim ma musayar fursunoni tsakanin Isra’ilan da kungiyar nan ta Hizbullah ta kasar Lebanon. A cikin watan Janairun wannan shekarar ne aka cim ma nasarar yin irin wannan musayar, sakamakon shiga tsakanin da Jamus ta yi. Peter Struck ya ce mahukuntan Isra’ilan sun bayyana gamsuwarsu da gudummuwar da Jamus ta bayar a wannan huskar:-

"Shugaban kasar Isra’ila da Firamiyanta sun bayyana godiyarsu ga taimakon da muka bayar, wato irin rawar da rundunar wsoji ta Bundeswehr ta taka a kan wannan batun. Mun dai yi iyakacin kokarinmu, wajen ba da taimakon da ya dace. Ina fatar cewa, za mu sami damar ba da wata gudummuwar kuma na gaba, inda tare da taimakon runudnar mayakan samanmu, za mu iya aiwatad da shirein musayar fursunoni."

Bayan tattaunawar da Peter Struck ya yi da mahukuntan Isra’ilan dai, ya kuma kai ziyara ne a tsohon garin birnin kudus. A yau ne dai ake sa ran zai gana da wata kungiyar dalibai, sa’annan kuma ya yi shawarwari da shugaban jam’iyyar adawa ta Labour, kuma tsohon Firamiya, Shimon Peres.