1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Su waye za su samu takarar APC?

May 13, 2026

Bayan shafe tsawon lokaci ana kai-kawo, jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na fitar da sunayen 'yan takarar da ta tantance wadanda za su taka rawa a zabukan da ke tafe.

Najeriya | APC | 'Yan Takara | Tantancewa
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, na shirin tantance 'yan takaraHoto: Ubale Musa/DW

Kimanin gwamnoni 20 ne dai, ko bayan 'yan majalisun dattawa 88 da na wakilai 242 ke zaman jiran sakamakon tantancewar  jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar. 'Yan takara kusan 3,000 ne dai, ke neman taka rawa a kujerun gwamnoni 28 da na majalisar dattawa 109 da majalisar wakilai mai maobobi 469 da ma kujera lamba daya wato ta shugaban kasa. An dai yamutse hazo cikin gidan APC, a kan yadda gwamnoni da ma jiga-jigan jam'iyyar suka rika sa kafa suna shure bukatun 'yan takara a matakai dabam-dabam.

Kokarin sulhu ya ci tura

Can a Rivers ga misali, jam'iyyar ta yi watsi da 'yan takara 65 da ke da alaka da gwamnan jihar  Siminalayi Fubara tare da tantance 33 na bangaren ministan Abuja Nysom Wike. A yayin da a  Yobe ma dai, aka gaza shawo kan bangarorin da ke fafatawa a kokarin neman mulkin jihar. Sakamakon da ke shirin fita ne dai, ke zaman zakaran gwajin dafi ga kokarin jam'iyyar na fitar da gwanin da ake shirin farawa daga ranar Jumma'a 15 ga watan. A jihohi da yawa kokarin sulhunta tsakani da kila dauki dorar gwamnoni dai ta rushe, sai dai kuma APC na tsoron abun da ke shirin ya faru kila bayan takarar fitar da gwanayen da ke da zafin gaske.

Har yanzu Mai Mala Buni ke rike da jam'iyyar APC

06:42

This browser does not support the video element.

Dokar zabe ta shekarar da ta shude ta haramta sauyin sheka tun daga farkon mako, to sai dai kuma da akwai tsoron zagon kasa cikin APC da tai cikar kwari da kuma kallon rikici cikin batun cika buri na takara. Abubakar Maikudi na zaman jigo a jam'iyyar, kuma ya ce fadin APC tana bukatar sauyi cikin salon tafi da harkokin zaben. Hakuri da runguma ta kaddara ko kuma kokarin zagon kasa cikin gidan na tsintsiya, duk da kokarin babakeren gwamnoni a APC ana ganin kokarin tantancewar da idanun matakin kawo tsafta a jam'iyyar.

Fancale, sakamakon rikicin cikin gida

A shekara ta 2023 dai, APC ta yi asarar gwamna a Zamfara a wani abun da ke zaman zagon kasa ga jam'iyyar. Kuma ko bayan nan, cikar kwari a APC na jawo damuwar da ke da girman gaske a batun takarar tsakanin 'ya'yanta. A ranar Jumma'a 15 ga watan Mayun 2026 ne za a fara zabukan fitar da gwani cikin gidan APC, shirin kuma da ke kokarin kare wa tare da samar da dan takarar shugaban ka sa ranar 23 ga watan na Mayun 2026 din. Matakin kuma da ke da burin raba gardama cikin gidan APC, bayan gaza kai wa ya zuwa sulhu tsakanin 'ya'ya.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani