1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Adawa da gwamnatin rikon kwarya

Mohammad Nasiru Awal RGB
April 12, 2019

Masu zanga-zanga sun yi fatali da sanarwar da sojoji suka bayar na cewa ba su da niyyar kafewa kan karagar mulkin kasar na lokaci mai tsawo, kwana guda bayan sun kifar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir.

Sudan Vizepräsident Awad Ibn Auf
Hoto: picture-alliance/Xinhua/M. Khidir

A cikin wata sanarwa da suka wallafa ta intanet, kungiyar Sudanese Professionals Association da ta jagoranci zanga-zangar adawa da Shugaba Omar Al-Bashir tsawon watanni hudu, ta bayyana alkawarin da majalisar mulkin rikon kwarya ta sojin ta yi da cewa yaudara ce, suna masu kira da a mika mulki nan-take ga hannun wata gwamnatin rikon kwarya ta farar hula. Sanarwar ta zo ne jim kadan bayan wani taron manema labarai da sabbin jagororin kasar suka yi a birnin Khartoum a wannan Juma'a.

Zanga-zangar adawa da gwamnatin rikon kwaryaHoto: picture-alliance/AP Photo

Da farko majalisar mulkin sojin ta yi alkawarin cewa kasar za ta samu gwamnatin farar hula, ta na mai cewa za a dauki shekaru biyu ana gudanar da shirye-shiryen zaben matukar za a guji shiga rudani. A taron manema labarai a birnin Khartoum, Janar Omar Zein Abedeen memba na majalisar mulkin rikon kwarya ya  ce, farar hula za su tafiyar da sabuwar gwamnatin Sudan.

A dangane da makomar shugaban da aka hambarar, ofishin kula da 'yancin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Sudan da ta hada kai da kotun hukunta laifukan yaki ta ICC wadda ta ba da sammacin kame al-Bashir bisa zargin aikata laifukan yaki shekaru 15 da suka gabata. Hakazalika shugabar ofishin 'yancin dan Adam na majalisar Michelle Bachelet ta yi kira ga mahukuntan Sudan da su saki dukkan mutanen da aka tsare saboda gudanar da zanga-zangar lumana, kana su gudanar da bincike kan amfani da karfi a kan masu zanga-zangar tun cikin watan Disamban bara. Sai da majalisar mulkin rikon kwaryar karkashin jagorancin ministan tsaro Mohammed Ahmed Awad Ibn Auf ta ce ba za ta mika al-Bashir ga kotun ta kasa da kasa ba.