Sudan: Al-Bashir ya saki fursunonin siyasa
April 10, 2018Talla
Tun a shekara ta 2015 Bashar ke gudanar da taruka da 'yan adawa da kungiyoyin 'yan tawayen kasar don kawo karshen yakin da aka jima ana gwabzawa a yankunan kasar. A na su bangaren kungiyoyin adawa sun bayyana cewar ya zuwa yanzu akwai sauran mutane 50 da ba su samu damar shakar iskar 'yanci ba ciki kuwa harda shahararren dan siyasar nan Mohamed Mokhtar al-Khatib jagoran jam'iyyar kwaminisanci.