1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turawa na fice daga Sudan

Ramatu Garba Baba MAB
April 23, 2023

Amirka ta kwashe jami'an kasar da iyalansu daga Sudan a yayin da aka shafe kwanaki tara ana gwabza fada a tsakanin sojin gwamnatin Sudan da dakarun RSF.

Jirgin ruwan Saudiyya da ya kwaso baki 'yan kasashen waje daga Sudan
Jirgin ruwan Saudiyya da ya kwaso baki 'yan kasashen waje daga SudanHoto: AL-IKHBARIYA TV/AFP

Britaniya ta bi sahun Amirka a kwashe jami'an diflomasiyyan kasar daga Sudan, in da ake ci gaba da barin wuta. Amirka ita ta soma aiki kwashe ilahirin ma'ikatan ofishin jakadancinta da ke Khartoum babban birnin kasar. A jawabinsa bayan kammala aikin kwashe ma'aikatan da iyalansu kusan dari daga cikin kasar, Shugaba Joe Biden na Amirkan ya ce, Amurka ta dakatar tare da rufe ofishin jakadancinta da ke Sudan a yanzu, in da daga bisani ya yi kira na a tsagaita bude wuta a fadan da ake gwabzawa.

Mahukuntan Saudiyya sun yi nasarar kwashe 'yan kasar daga Khartoum in da fadan ya fi zafi a yayin da rahotanni ke cewa, mutum sama da dari hudu sun rasa rayukansu a fafutukar kifar da gwamnatin Abdel Fattah al-Burhan a fadan da aka kwashi kwanaki tara yanzu ana gwabzawa.