Amirka za ta tura jakadanta Khartoum
December 4, 2019Talla
An dai kamo hanyar gyara dangantaka tsakanin Amirka da Sudan biyo bayan hambarar da gwamnatin kama karya na Omar al-Bashir kafin a girka sabuwar gwamnatin hadaka.
Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ne ya sanar da wannan ci gaban, a yayin wata ganawa da Firaiministan kasar ta Sudan Abdallah Hamdok da ya kai ziyara fadar WhiteHouse a wannan Laraba. Wannan shi ne karon farko da ake samun hakan a tsakanin kasashen biyu a tsawon shekaru 23.