An ji amon fashe-fashe a birnin Khartoum na Sudan
November 8, 2025
Shaidu sun ce jirage marasa matuka ne suka harba rokokin da suka jawo fashe fashen a gundumar Umdurman kusa da barikin soji da kuma kan tashar samar da wutar lantarkin da ke yankin, lamarin da ya jawo daukewar lantarki.
Rundunar sojin kasar ta ce garkuwar makamanta ta harbor gwamman jirage marasa matuka da suka yi kokarin kai hare hare kan sansanonin soji da filin jirgin sama na birnin Khartoum, ba a dai samu asarar rayuka ba .Kamar yadda rundunar sojin ta ce ta kakkabo gwamman jirage marasa matuka a yankin Atbara da ke da tazarar kilomita 300 daga birnin Khartoum.
Karin Bayani: Sudan: Za a kawo karshen yakin basasa?
Hakan dai na zuwa ne, kwana guda bayan da mayakan RSF suka sanar da amincewarsu da shirin tsagaita wuta na kwanaki 30 da Amurkan ta gabatar da ake sa ran zai taimaka wajen shigar da kayyakin agaji
Sai dai a hannu guda, shugaban hukumar sojin Sudan Janar Al Burhan wanda ya yi fatali da batun tsagaita wutar, ya nemi yan kasar, maza da mata su daura damarar yakar wadanda ya siffanta da dodanni mashaya jinin bil adama:
Karin Bayani: Amurka ta kudiri aniyar kawo karshen yakin Sudan
"Za muci gaba da fatattakar wadannan makiya al'ummar Sudan da ke musu kisan kiyashi babu kakkautawa. Baza mu saurari duk wani kiran sasantawa ko sassauta musu ba. Domin yin hakan cin amanar mutanen da wadannan miyagun suka kashe ne. Mun yi ammanar cewa, albarkacin hadin kai da daukin da kuke kawowa rundunar soji daga ko ina, za muyi nasara kansu ba da jimawa ba.”
Tuni dai mutane a garuruwa suka amsa kiran Janar Al Burhan na daura damarar yakar yan tawayen RSF kamar yadda mahalarta wannan gangamin yakin a birnin Gadhareef ke fadi:
Karin Bayani: Dakarun RSF a Sudan amince da kudurin sulhu
"Mun fito mazanmu da matanmu matasanmu da tsoffinmu don sadaukar da rayukanmu kan manufar kare al'ummar Sudan da tabbatar da ganin mun fattaki mayakan RSF na Janjaweed daga birnin el fasheer da ma dukkanin Sudan.”
Tuni wasu fitattun yan siyasar kasar irin su Dr Tijjani Alhusain suka fara nuna fargabarsu ta yiwuwar darewar kasar, muddin bangarorin basu amince da zama kan teburin shawara don kawo karshen rikicin ba:
"A kwai yiwuwar sake raba Sudan gida biyu muddin sojoji za su ci gaba da tunanin za su iya murkushe yan tawaye baki dayansu da karfin tuwo, bayan kwashe fiye da shekaru biyu suna yaki da juna. Muna kira ga jagororin jama'a da su yi hattara, kar ya kaimu ga sake ballewar wani bangaren na Sudan.”