Tsugune bata kare ba a Sudan
May 11, 2019Talla
Dubban masu zanga-zanga nedai suka kafa sansaninsu a wajen ginin headkwatar rundunar soji da ke tsakiyar birnin Khartoum, inda suka lashi takobin tursasawa shugaban mulkin sojin yin murabus, kamar yadda suka tusa keyar Al-Bashir.
Al'ummar Sudan din a cewar daya daga cikin masu zanga zangar zaman dirshan din mai sunaIman Hussein, sai sun ga abunda ya turewa buzu nadi dangane da kafuwar gwamnatin farar hula, wanda suka fara tun ranar 6 ga watan Afrilu.
Da farko dai gangamin na korar Al-Bashir ne, yanzu kuma ya rikide zuwa na korar wadanda suka taimaka wajen kifar da Al-Bashir din a ranar 11 ga watan Afrilu.