Jaridun Jamus: Sudan da Mali sun dau hankali
November 29, 2024Za mu fara sharhunan da jaridar die tageszeitung wace ta duba siyasar kasar Mali. Inda jaridar ta ce bayan sukar da ba a saba gani ba game da ci gaban siyasar Mali, an kori firaministan rikon kwarya Choguel Maiga tare da maye gurbinsa da wani janar mai biyayya ga tsarin sojojin da ke mulki. Don haka an bar rukunin siyasa na farar hula. Shekaru hudu bayan faduwar zababbiyar gwamnatin farar hula ta Mali, an kammala mika kasar ga hannun soja. An nada sabon firaministan wanda baya daya daga cikin fitattun fuskokin gwamnatin mulkin soja a matsayin ministan kula da yankuna, tun daga lokacin ya aza mukarrabansa a wasu manyan mukamai.
Sai kuma jaridar Der Tagesspiegel wacce ta ce, yunwa na ci gaba da hallaka mutane a Sudan. A cewar jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan a yanzu ana fama da matsananciyar yunwa a sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam, inda tun watan Agusta ake kokarin isa ga sansanin amma ba hali duk da yunwar da suke fuskanta. Yanzu a karshe agaji ya isa a karon farko cikin watanni, kimanin mutane miliyan daya a sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a yankin Darfur na yammacin Sudan sun sake samun tallafin abinci. Kamar yadda Shirin Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya sanar, wasu ayarin motocin daukar kaya guda biyu dauke da abinci sun isa babban sansanin da ke gefen birnin El Fasher da ke fama da rikici.
Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi nazari kan halin da ke ciki a kasar Mozambique tana mai cewa, rashin nasara a kokarin tattauna rikicin siyasar a Mozambique ya hana madugun 'yan adawa Venâncio Mondlane da shugaba Filipe Nyusi shawo kan matsalar da ke kara kamari tun bayan sanar da sakamakon zabe. Shugaban kasar ta Mozambique mai barin gado Filipe Nyusi ya fara kokarin warware rikicin kasarsa, ta hanyar tattaunawa. Da farko dai ya gayyaci daukacin 'yan takara hudu a zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar tara ga watan Oktoba zuwa wani taro, domin shawo kan tashe-tashen hankula wadanda suka mamaye kasarsa. Sai dai kawo yanzu, babu wata ganawa da babban madugun 'yan adawa Venâncio Mondlane wanda ke kasar waje saboda dalilai na tsaro.