Sudan da Sudan ta Kudu sun fara yunkurin yin sulhu
January 28, 2012Sudan a wannan asabar ta ce zata sako duk jiragen danyen man Sudan ta Kudu da ta ke rike da su domin sassauta rikicin da ke tsakaninsu ta yadda zasu cigaba da gudanar da yarjeniyoyin da ke daukan tsawon lokaci yanzu. Said Khatib mai magana a madadin wakilan Sudan ya ce wannan mataki da suka dauka ya nuna cewa a shirye suke su koma teburin tattaunawa. Jiragen ruwa uku wadanda ke dauke da kimanin garewanin mai sama da milliyan biyu suka makale a tashar ruwan Sudan, abun da kuma ya kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan da suka shafi tattalin arzikin Juba wanda ke dogaro kan kashi 90 cikin 100 na kudin shigowar man fetur. Ita dai Sudan ta Kudu tana zargin Sudan da sace mata danyen mai na kimanin dala milliyan dari takwas da goma sha biyar, to sai dai gwamnati a Khartoum ta ce ta karbi man ne a matsayin kudaden shigar da man da ta yi wa Sudan ta Kudun.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal