Mutum sama da 100 sun mutu
September 9, 2020Talla
Gwamnatin Khartoum ta sanar da ware dalar Amurka kusan miliyan uku, domin taimakawa wadanda wannan bala'i daga indallahi ya ritsa da su, a cewar kamfanin dillancin labaru na kasar.
A yayin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce, da taimakon masarautar Hadaddiyyar Daular Larabawa, ta samu nasarar aikewa da Tones 100 na kayan agaji ciki har da Barguna, domin rabawa a jihohi 12 na Sudan din.
Ambaliyar kogin na Nilu dai, ya yi sanadiyyar rayukan mutane 102, a yayin da dubban daruruwan gidaje suka salwanta, a cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Khartoum. Tuni gwamnati ta ayyana da dokar ta baci na tsawon watanni uku.