Sudan: Dokar yaki da bakin haure zuwa Turai
December 12, 2016Duk da hadin gwiwar da ta yi da Tarayyar Turai kan yaki da matsalar kwararar bakin haure dake keta kasarta zuwa wasu kasashen, kasar Sudan na ci gaba da fama da matsalar masu fasa kwaurin mutane, lamarin da ya sanyata kaddamar da wasu sabin dokoki masu tsauri don magance matsalar.
Ma'aikatar shige da fice ta kasar ta Sudan dai ta ce a yanzu haka, a cikin kasar ta Sudan, akwai kimani bakin haure miliyan uku, da suka fito daga kasashen daban-daban na Afirka, wadanda suka gama daure kayansu suna jiran samun dammar tsallakewa zuwa Turai ko wasu kasashen na daban, in ji kakakin ma'aikatar Usamah Atrash:
"Duk da shirin musamman da mukai wa Hamadar Yammacin Afirka, na sa ido ba kakkautawa, tare da hadin gwiwa da Tarayyar Turai, kungiyoyin da ke fasa kwaurin mutane sun kusan gagararmu, sabi da sauya salo da dabarun da suke yi a kai-a kai, da kuma barbaza yaransu da suka riga suka yi a ko ina a fadin Sudan"
Fatimah Waleed Abdu, wata 'yar kasar Mali, na daya daga cikin wadanda suka fada hanun masu fasa kwaurin mutanan da suka karbi 'yan kudadenta, kan za su kaita Turai, amma suka 'yar da ita a Saharar kasar ta Sudan:
"Dole ce ta sanyani tsallakewa na bar kasata, don kar a ci zarafina, kuma ina tsoron abin da zai iya faruwa ga 'ya'yana. Na zo nan ne,saboda an ce mana akwai saukin zuwa Turai daga nan. Bayan irin tashin hankalin da na gani a gida, bani da aniyar komawa"
Thomas Kazaki, wani dan kasar Laberiya da ya zo kasar ta Sudan kan hanyarsa ta zuwa Isra'ila na daya daga cikin irin wadannan bakin haure da suke makale a Sudan:
"Komawa gida ma shi kansa a yanzu yana da matukar wuya. Duk kudaden hannunmu sun kare. Akwai wadanda suke zaune da jinya ba sa iya zuwa asibiti saboda rashin kudi. Adadinmu, mu 'yan laberiya a nan mun kai kimanin 500."
Kasar ta Sudan dai, ta ce ta tashi haikan wajen yaki da masu fasa kwaurin 'yan ci ranin, ta hanyar sanya tsauraran dokoki, ciki har da hukuncin kisa. To sai dai kamar yadda Muhammad Taha, kwararre kan laifufuka ke gani, sanya tsagwaron doka ba za su iya hana fasa kaurin mutanan ba.
"Dole ne sai an yi amfani da fasahar na'urar zamani don sa ido a hada-hadar bankuna da kuma ture-turen kudade ta shafukan sadarwa. Ya zama wajibi a sa ido don bankado batagari daga su kansu jami'an yaki da fasa kwaurin. Domin manyan hanyoyin da ake samun yin fasa kwaurin mutane guda biyu ne, ko dai a ba wa jami'in tsaro toshiyar baki, ko kuma ta hanyar halatta kudaden haram."