Makomar Sudan bayan murabus din Hamdok
January 5, 2022Al'ummar Sudan din dai na ci gaba da yin bore na nuna kyama ga gwamnatin wucin gadi ta mulkin soji kwanaki kalilan bayan marabus din da Firaminista Abdlla Hamdok ya yi. Kawo yanzu ra'ayoyi na cin karo da juna a tsakanin al'ummar kasar a game da marabus din, inda yayin da wasu ke kira ga masu rajin kishin dimukuradiyya da su yi amfani da murabus din Hamdok din su hada hannu waje guda, wasu kuwa fargaba suke nunawa kan yiwuwar sojojin Sudan din su yi amfani da damar su kuma karbe mulkin kasar. Ana dai fargabar sojojin ka iya yin kane-kane a cikin harkokin mulki ta hanyar nada firaministan da suke so kuma suka zaba, abin da zai iya zama tsaiko ga kokarin kai wa ga gaci na samar da mulkin dimukuradiyya da ake fafutukar nema.
Karin Bayani: 'Yan Sudan sun fito zanga-zangar kifar da sojoji
Abdalla Hamdok na daga cikin mambobin gwamnatin sojoji da farar hula ta wucin gadi da aka kafa a shekara ta 2019, bayan faduwar gwamnatin Omar al-Bashir. Gwamnatin da aka aza kyakkyawan fata a kanta na samar da hanyoyin kafuwar mulkin dimukuradiyya a Sudan, ta samu goyon bayan kasashen duniya sakamakon alwashin da ta sha tun da farko na shirya sabon zabe kafin shekara ta 2023. Sai dai ba a yi nisa ba aka kifar da gwamnatin ta wucin gadi a cikin watan Oktobar bara, wanda a cikin juyin mulkin sojojin suka yi ruwa suka yi tsaki suka kori duk wani farar hula a cikin gwamnatin har da Firaminista Hamdok. To amma bayan wata guda firaministan da akai wa daurin talala ya sake dawowa kan madafun iko, sakamakon yarjejniyar da suka yi da sojojin a ranar 21 ga watan Nuwambar bara a karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan jagoran juyin mulkin na Sudan.
A kwana a tashi al'ummar ta Sudan ta sake tsunduma cikin sabon bore bayan da Hamdok ya cimma yarjejeniya da sojoji, a ganinsu shi da sojojin kusan bakinsu daya. A ganinsu, babu aniyar mika mulkin ga farar hula kafin 2023. Christine Felice Roehrs daraktan gidauniyar Friedrich Ebert Stiftung reshen Sudan da ke Khartum babban birnin kasar, ta ce firaministan ya ce ya yi marabus ne saboda ya dakatar da zubar da jinin al'umma. Abdallah Hamdok ya shiga halin tsaka mai wuya, dole ce kanwar naki ta tilasta masa yin marabus saboda daukacin kungiyoyin farar hula masu fafutukr neman sauyi a Sudan na FFC wadanda suka kasance cikin gwamnatin rikon kwarya sun ki amincewa da yarjejeniyar da ya cimma tare da sojoji inda suke masa kallon zama yaron sojojin.
Karin Bayani: Zanga-zangar adawa da juyin mulki a Sudan
Theodore Murphy shi ne daraktan kula da tsare-tae na Afirka na kwamitin gudanarwa na kungiar Tarayyar Turai, kuma a ganinsa abu na farko shi ne a samu gwamnatin hadin kan kasa tsakanin farar hula da sojoji: sai dai kuma a cewarsa abubuwa sun rikice ta yadda masu zanga-zangar ke neman sojoin su fice daga cikin gwamnati su bar farar hula zalla, abin da ya ce yana tunanin kasashen duniya na ganin daidai ne. Galibin sojojin da ke rike da mulki a Sudan, sun yi aki a karkashin tsohuwar gwamnatin Omar al-Bashir wanda masu neman sauyin suke ganin har yanzu ba ta canza zani ba a fafutukar da ake yi ta neman sauyi. A cikin irin wannan rudani da aka shiga a Sudan ana ci gaba da samun salwantar rayuka, inda kawo yanzu sama da mutane 57 masu zanga-zangar suka mutu.